Bom ya jikkata wasu a taron gangami na Jam’iyyar APC a filin Ojukwu da ke Fatakwal.

0
31

Mutane 3 ne suka jikkata sakamakon wasu bama-bamai biyu da ake zargin sun tarwatsa taron gangamin jam’iyyar APC a filin wasa na Rumu-Woji, da aka fi sani da filin Ojukwu, a Fatakwal.

Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ba ta mayar da martani kan lamarin ba duk da cewa wurin taron ya raba shinge da ofishin ‘yan sanda na Mile 1.

Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC reshen Jihar Ribas, Darlington Nwauju, wanda ya raba hotunan wasu mata biyu da abin ya shafa ya ce, “Rana ce ta bakar rana a tarihin dimokuradiyya, inda ake amfani da dabaru iri-iri don dakile jam’iyyun siyasa na adawa a Jihar Ribas.

“Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Monguno, shugaban DSS da IGP Usman Alkali dole ne su jajirce kan jihar Ribas su kawar da rikicin siyasa. Babu wani dan siyasar adawa guda daya da zai tsira. Mun kuma kama wasu sahihan bayanan sirri na shirin kai wa manyan ‘yan siyasa hari a jihar .

 

Daga Fatima Abubakar.