DA DUMI DUMI: Kotu ta yanke wa dan sanda Vandi hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kisan Bolanle Raheem

0
28

Babbar kotun jihar Legas da ke zama a dandalin Tafawa Balewa annex, Igbosere, tsibirin Legas ta yanke ma wani mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP) hukuncin kisa ta hanyar rataya, Vandi bisa laifin kashe wata lauya ‘yar Legas Mrs Omobolanle Raheem.

Mai shari’a Ibironke Harrison ya bayyana cewa, masu gabatar da kara, gwamnatin jihar Legas, ta tabbatar da tuhumar da ake yi wa mai laifin ba tare da wata shakka ba.

“Kotu ta samu wanda ake tuhuma da laifin aikata kisan kai. Za a rataye ka a wuya har ka mutu.” alkali ya bayyana.

A ranar 16 ga watan Janairu ne gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da Vandi a gaban kotu bisa laifin harbe wata lauya mai juna biyu mai shekaru 41 da haihuwa a shingen binciken gadar Ajah a ranar 25 ga watan Disamba, 2022.

Mai laifin ya fuskanci tuhuma guda daya da laifin kisan kai sabanin sashe na 223 na dokar manyan laifuka ta jihar Legas, 2015.

Firdausi Musa Dantsoho