Gwamnatin Jihar Kano Ta Rufe Asibitin Da Ke Da Ma’aikata Biyu

0
24

Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu ta jihar Kano (PHIMA) ta rufe wani asibiti mai zaman kansa mai suna Choice Clinic mai ma’aikata biyu kacal, ma’aikacin jinya da kuma mai shara.

Jaridar This newspaper  ta ba da rahoton cewa rufewar yana zuwa ne kawai mako guda bayan hukumar ta rufe asibitin Reach saboda karya dokokinta da daidaitattun ka’idojin aiki.

Da yake jawabi bayan rufe cibiyar, Darakta Janar na hukumar, Farfesa Salisu Ibrahim Ahmad, ya ce asibitin Choice Clinic ya samu sabani da wani asibitin da suke gina ginin guda daya “wanda muka lura suna gudanar da ayyukansu ba bisa ka’ida ba.

Ya bayyana cewa lamarin ya baiwa hukumar damar soke rajistar su tare da umarce su da su samu wani wuri a ko’ina a jihar don sake bude cibiyoyin bayan tantancewar da PHIMA ta yi musu.

Ya ce, “A Rijiyar Zaki, dayar cibiyar ta rufe kamar yadda muka ba da umarni. Abin takaici, asibitin Choice ya ƙi dakatar da aiki, Da muka isa wurin sai muka samu wata mata a asibiti saboda anyi mata aiki, Don haka, mun jinkirta kulle cibiyar har sai da aka sallame ta. Amma mun rufe dakin theatre. Mun ba su makonni biyu su dakatar da ayyukansu, amma sun ki bin umarninmu.

“Mun je can muka rufe shi….Wannan saboda ba su da likita; babu mai harhada magunguna da sauran ma’aikatan da suka wajaba don isar da sabis na kiwon lafiya. Suna da ma’aikata biyu ne kawai, ma’aikaciyar jinya da mai shara.”

Firdausi Musa Dantsoho