DA DUMI-DUMI: ‘Yan sanda a babban birnin tarayya sun kubutar da yan uwan Nabeeha Al-Kadiriya da aka yi garkuwa da su a BWARI.

0
30

Kamar yadda CP yayi alƙawarin samar da ingantaccen tsarin tsaro a yankunan da abin ya shafa, bayan .

Biyo bayan ci gaba da gudanar da aiki da  rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ke yi don yaki da masu garkuwa da mutane tare da hadin guiwar dakarun sojojin Najeriya, a kan sahun masu garkuwa da mutane da suka afkawa yankin Zuma 1 da ke karamar hukumar Bwari a ranar 2 ga watan Janairun 2024.

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ceto wadanda lamarin ya shafa tare da hada su da iyalansu .

Jami’an sun yi nasarar ceto wadanda abin ya shafa a dajin kajuru a jihar Kaduna da misalin karfe 11:30 na daren ranar Asabar 20 ga watan Janairun 2024.

Yayin da yake yabawa,Sufeto Janar na ‘yan sanda IGP Olukayode Egbetokun ph.D., NPM, bisa tura sabuwar runduna ta musamman da aka tanada don yaki da yan ta’adda , wanda ya ba da kwarin gwiwa ga tsarin tsaro na FCT  kuma hakan ya sa jama’a su aminta da shi ,

Kwamishinan Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, CP Haruna G. Garba psc, na fatan sake jaddada aniyar rundunar na ci gaba da aikin samar da tsaro a yankin da sauran sassan yankin domin tabbatar da zaman lafiya ga kowa da kowa.

Don haka ana ƙarfafa mutanen FCT nagari su lura da waɗannan layukan gaggawa da rundunar ta wallafa kamar haka.

08032003913, 08061581938, 07057337653, da 08028940883.
PCB: 09022222352

Wannan sakon na zuwa ne daga Jami’a na Hulda da jama’a na rundunar Yan Sandan  SP Josephine Adeh, Anipr
Domin: Kwamishinan ‘Yan Sanda
Rundunar ‘yan sandan FCT.

Daga Fatima Abubakar.