Hukuncin Kotun ƙoli ya haifar da Rikici a Jihar Nasarawa

0
7

Hukuncin Kotun ƙoli: Rikici ya ɓarke a Nasarawa akan ƙin amincewa da hukuncin

Hukuncin Kotun Koli ya jefa al’umma damuwa yayin da mazauna garin Nasarawa suka yi zanga-zanga, tare da tare hanyoyi a Jihar.

A halin yanzu dai rikici ya barke a jihar Nasarawa kan hukuncin kotun koli da ta tabbatar da zaben gwamna Abdullahi Sule a matsayin halastaccen Gwamnan Jihar.

Jaridar Tozali ta rawaito cewa a yau Juma’a kotun koli ta tabbatarwa Gwamna Sule kujerarsa ta Gwamna, inda yanzu ta tabbatar da shi a matsayin zababben Gwamnan Jihar.

Sai dai hukuncin bai yi wa wasu mazauna Jihar daɗi ba, musamman magoya bayan Jam’iyyar PDP inda suka tare manyan tituna domin nuna adawa da hukuncin kotun kolin.

Babban Titin Lafia zuwa Jos mai cike da cunkoson Jama’a, sun toshe shi gaba ɗaya yayin da masu zanga-zangar suka kona tayoyi a gaban sakatariyar Jam’iyyar ta Jihar inda suka tare hanyar.

Duk da cewa jami’an tsaro na kokarin dawo da zaman lafiya, amma zanga-zangar ta tilastawa masu ababen hawa yin amfani da wasu hanyoyi daban-daban a cikin garin Lafia babban birnin Jiha domin tafiya inda su ka nufa.

Lokacin da Wakilin mu ya tuntuɓi Jami’in hulɗa da Jama a na ‘yan sanda reshen Jihar Ramhan Nansel yayi gajeran bayani kan “Jihar Lafia ba ta da wata matsala daga nan bai sake cewa komai ba.”

 

 

Hafsat Ibrahim