Muke da yawan Jama a , a Arewa yakamata madafun iko su zamto a yankunan mu- Farfesa Sadiq Umar Abubakar Gombe.

0
7

Shirin Gyara kayanka

Tare da Muhammad sani

 

Inda suka tattauna kan al amuran da suka Shafi Arewancin Najeriya .

Babban daraktan gudanarwa Ferfesa Sadiq Umar Abubakar Gombe wato ( Deputy Director General operations) Wanda Masani Kuma Mai fashin Baki kan al amuran yau da kullum ,a zantawar shi da wakilin Tozali cikin shirin gyara kayanka inda suka tattauna kan al’amuran rashin tsaro da arewacin najeriya ke fuskanta ya bayyana cewa kalubalen da yankin Arewa ke fuskanta ya samo asaline daga baragurbin shuwagabanni da manyan jam’iyyun arewa ke wakiltawa zuwa majalisa da zababbun sanatoci, hakan ya sanya basa iya kawowa yankunan su cigaba.

Ya kara da cewa lokaci yayi da jam’iyyun arewa zasu bar adawa su koma cancanta, hakan zai farune tun daga matakin zaben dan takara wato primary election,ya zamto dan takara daya arewa zata ware a maimakon jam’iyyun kowacce ta fitar da dan takarar ta, wanda hakan koma bayane tare da rarrabakan yan Arewa a matsayin yanki Guda.

A damokradiyya yawan Al’umma shike tasiri, sannan ya bayyana raayinsa kan dauke wasu ofisoshin Babban banki Wanda hakan a ganin sa mu Yan Arewa muke da yawan sanatoci da Yanmajalisu wadanda suke da fifiko a bangaren zartar wa, wannan zai sa mu zamto a gaba a maimakon mune koma baya, kenan sanatocin mu albashinsu suke yiwa sannan ga wakilanmu sun maida hankali ga motocin da ake basu suna hawa wanda shi ya sanya ba sa iya hana wani, ko kawowa yan Arewa Wani muhimmin cigaba kokuma yaunkurin hana abinda barin shi yankin su koma baya ne ga yankin ,sannan ace baza a rinki bamu fifiko a al’amuran cigaba ba.

Lokaci yayi da matasan arewa domin mu dattijawan Arewa kullum muna fafutukar hana duk Wani koma baya a yankunan mu. Amman yanzu lokacine na matasa kuma muna kira a garesu da su farka

Wakilai Dari da chasain muke dasu a Arewa , saboda haka duk wani mataki na rinjaye mune muke da su Sannan Jihohin mu sunfi yawa.

Batun kwashe wasu daga cikin ofisoshin Babban banki da ake céwa za a kwashe zuwa jihar Legos sunanan akan bakansu.Amman raayi hukumar kula da tashi da daukar jirage ta FAAN na cewa taji dadin komawar ta jihar Legos ra’ayin tane.

Amman daga karshe ya bayyana raayinsu na Dattawan Arewa na rashin goyan bayan duk Wani kadara daza a dauke daga Arewacin a maidashi kudanci.

Kasance da Shirin gyara kayanka na wannan satin na tashar Tozali TV inda zakuji cikakken Shirin . Tare da Abokin tattaunawar.

 

 

Hafsat Ibrahim