DA DUMI DUMIN TA:Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da kara kwanaki goma don canjin tsofaffin takardun naira 200,500 da 1000 daya.

0
66

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da tsawaita wa’adin kwanaki 10 na musayar kudade zuwa sabbin takardun kudi.

Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar a garin Daura na jihar Katsina.

Emefiele, wanda ke Daura a safiyar Lahadi, ya yi ganawar sirri da shugaba Buhari, inda ya samu amincewar sa.

Ya ce ’yan Najeriya da har yanzu ba su sauya takardar kudin Naira daga tsohuwar zuwa sababbi ba, yanzu suna da damar yin hakan.

Gwamnan babban bankin ya yi gargadin cewa dole ne mutane su yi amfani da damar domin ba za a kara tsawaita wa’adin ba.

A shekarar da ta gabata ne,Babban Bankin kasar ya gabatar da sabon tsarin takardar kudi na Naira 200, 500 da 1000 tare da bayar da wa’adin ranar 31 ga watan Janairu, 2023 don musanya takardun kudin.

 Sai dai kuma ‘yan kasar ba su samu saukin samun sabbin takardun kudi daga bankunan kasuwanci ba, lamarin da ya sa jama’a suka koka da neman a kara wa’adin.

 Cikakkun bayanai daga baya….

 

Daga Fatima Abubakar.