DA DUMI-DUMINSA: INEC ta tsayar da ranar zabe a Kebbi, Adamawa, da sauran zabuka da ba’a kamala ba

0
51

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanya ranar Asabar 15 ga watan Afrilu domin gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi.

 

News Point Nigeria ta ruwaito cewa, hukumar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin.

 

“Sakamakon taron da ta gudanar a yau, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta yanke shawarar cewa za a gudanar da dukkan manyan zabukan gwamnoni, na kasa da na ‘yan majalisar jiha a ranar Asabar 15 ga Afrilu, 2023.

 

“Sanarwar hukuma za ta biyo baya nan ba da jimawa ba,” in ji tweet din.

Sanarwar ta zo ne mako guda bayan zaben gwamnonin jihohin Kebbi da Adamawa da aka bayyana cewa bai kammalu ba.

 

A ranar Litinin din da ta gabata ne aka bayyana zaben da aka yi a Kebbi ba a kammala shi ba, sakamakon saba dokokin zabe da ya kai ga soke sakamakon zabe a kananan hukumomi 20 daga cikin kananan hukumomi 21 na jihar.

 

Jami’in zabe na INEC a jihar, Farfesa Yusuf Sa’idu, ya ce tashe-tashen hankula, lalata kayayyakin zabe, dagula harkokin zabe da kuma yawan kuri’u sun taka rawa wajen ganin zaben bai kammalu ba.

 

Kafin a ce zaben bai kammala ba, jam’iyyar APC ce ke kan gaba da kuri’u 388,258, yayin da PDP ta samu kuri’u 342,980.

 

A Adamawa ‘yar takarar jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru (aka Binani) ta samu kuri’u 390,275 yayin da gwamna mai ci Ahmadu Fintiri da dan takarar PDP suka samu kuri’u 421,524.

 

Sai dai jami’in tattara bayanai na INEC a jihar, Farfesa Muhammadu Mele na Jami’ar Maiduguri, ya bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba saboda ratar kuri’u.

 

Ya ce, “Ba a gudanar da zabe a unguwanni 47 ba, wanda ya shafi rumfunan zabe 69. Don haka, wannan ya ba mu tazarar 31,249. Adadin PVC da aka karba a wuraren da ba a yi zabe ba ya kai 37,016.”

 

Firdausi Musa Dantsoho