Da duminsa: Kotu ta tsige Abba Yusuf na NNPP a matsayin gwamnan Kano

0
26

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kano ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ta bayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Nasiru Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana Yusuf wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) a matsayin wanda ya lashe zaben bayan kammala zaben watan Maris.

Kotun ta cire kuri’u 165,663 daga jimillar kuri’un da Gwamna Yusuf ya samu a kan cewa katin zabe (165,663) ba a buga tambari ko sanya hannu ba, don haka aka bayyana cewa ba su da inganci.

Karin bayani ba da jimawa ba…