Yanzu Yanzu Rundunar Yan sandan jihar kano ta sanya dokar tabaci a fadin Jihar.

0
9

Yanzu Yanzu Rundunar Yan sandan jihar kano ta sanya dokar tabaci a fadin Jihar

Rundunar yan sandan jihar Kano ta Sanya dokar hana shige da fita a fadin Jihar na tashon awa 24, domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma . Acewar Rundunar tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi. Al Umma alhakin yin hakan ya rataye a wuyansu a matsayinsu na Jami an tsaron

Wannan tafito ta cikin wata sanarwa da Rundunar ta aikewa manema labarai. Sannan ya kara dacewa Ya kamata al’ummarta jihar kano su sani tuni mun baza jami’an tsaro a lungu da sakon na jihar kano domin tabbatar da cewa al’umma sun bi wannan doka ta hana fita tsahon awa 24″

Tozali TV ta rawaito cewa Kwamishinan Yan Sanda na jihar kano CP Muhammad Usaini Gumal ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu gabanin bayyana sakamakon kotu.

Sanarwar tace dokar ta fara aiki daga karfe 6 na yammacin Laraba, 20 ga Satumba zuwa karfe 6 na yammacin Alhamis, 21 ga Satumba, 2023. Kuma za’a hukunta duk wanda aka samu ya karya wannan doka. .

 

Daga Fatima Abubakar.