Firaministan Chadi kuma shugaban ‘yan adawa Succes Masra ya yi murabus.

0
21

Masra ya miƙa takardar ajiye aikin ne a ranar Laraba.

“Kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada, a yau na miƙa takardar ajiye aikina da kuma ta gwamnatin riƙo wadda a yanzu ta zama ba ta da amfani bayan kammala zaɓen shugaban ƙasa a ranar 6 ga watan Mayu,” kamar yadda Masra ya wallafa a shafinsa na X.

 

Masra ya yi fice a matsayinsa na ɗan adawar gwamnatin mulkin soji wadda ta samu mulki a watan Afrilun shekarar 2021.

 

An nada shi a matsayin firaministan gwamnatin rikon kwarya a watan Janairu, watanni hudu gabannin zaben, a wani mataki na faranta wa ‘yan adawar ƙasar.

 

A cikin watan Maris ne aka amince da takararsa a zaben shugaban kasa don mayar da kasar bisa tsarin mulkin dimokuradiyya.

 

Kasar wadda ke da arziƙin mai ita ce ta farko a jerin ƙasashen da aka yi juyin mulki a yankin Sahel na Yamma da Tsakiyar Afirka da ta yi irin wannan yunƙurin.

 

Kafin a sanar da sakamakon wucin-gadi na zaɓen a hukumance, Masra ya yi ikirarin samun nasara, yana mai zargin cewa ana shirin magudin zabe.

 

Sai dai daga baya Hukumar Zaben Chadi ta ce Deby ya lashe zaben ne kai tsaye da kashi 61% na kuri’un da aka kada kuma majalisar tsarin mulkin kasar ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Firaministan Chadi kuma shugaban ‘yan adawa Succes Masra ya miƙa takardar ajiye aiki bayan shugaban ƙasar mai ci Mahamat Idriss Deby ya yi nasara a zaɓen da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu.

 

Hafsat Ibrahim