Har yanzu ana zaman dari-dari a kasuwar banex plaza dake Abuja.

0
14

Da yake mayar da martani game da lamarin a ranar Talata, kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa an rufe kasuwar ne na wucin gadi domin a kamo wadanda suka haddasa rikicin.

 

Manjo-Janar Nwachukwu ya ce yana da kyau a lura cewa sojojin da aka lakada wa dukan ba su dauke da makami kuma ba su aikata wani abu na wuce gona da iri da ke barazana ga wani ba.

 

Ya kara da cewa, zaluncin da aka yi musu bai dace ba, kuma “Har yanzu ba a kamo wadanda suka haddasa rikicin na Banex Plaza ba.

 

“Lamarin na bukatar a zurfafa gudanar bincike a wurin da abin ya faru, don gano musabbabin faruwar lamarin.

 

“Ana sa ran a karshe binciken zai tabbatar da tsaro a Abuja da kuma hana faruwar irin haka a nan gaba ga sojoji da sauran jami’an tsaro, kamar yadda aka gani a wasu wurare,” in ji Nwachukwu.

 

Babban jami’in sojan ya yi kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen mu’amala da sojoji da sauran jami’an tsaro, musamman a lokacin da suke cikin kaki.

 

Ya ce akwai hanyoyin da za a iya kai karar sojoji idan sun yi wani laifi ko rashin da’a ga hukumomin da suka dace.

 

A cewarsa, ya zama wajibi a yi amfani da wadannan hanyoyi wajen tabbatar da zaman lafiya da mutunta masu yi wa al’ummarmu hidima

 

 

 

Hafsat Ibrahim