Gudanar Da Mulki A Zamanance: Jihar Gombe Ta Sha Ruwan Lambobin Yabo.

0
23

…Yayin Da GOGIS Ta Zama Zakara A Tsarin Taswira Da Zamanantar Da Harkokin Filaye.

…Hukumar Tabbatar Da Bin Ƙa’idoji Da Tsare-Tsare Na Gombe Kuma Ya Yi Fice A Fagen Samar Da Tsare-Tsaren Zamani

…GSU Kuwa Ta Zama Jami’ar Jiha Mafi Fice A Harkokin Yanar Gizo

Jihar Gombe ta sha ruwan kyaututtuka da lambobin karramawa yayin da Fadar Shugaban Ƙasa, ta hannun Hukumar Kawo Sauye-Sauye ga Harkokin Gwamnati (BPR) ta baiwa hukumomin gwamnati da ɗaiɗaikun jama’a lambobin yabo bisa gagarumin nasarorin da suka cimma a fannonin fasaha da ƙere-ƙere.

A wani gagarumin biki da aka gudanar a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa dake Abuja, Jihar Gombe ta yi fintinkau ga manyan hukumomin tarayya dana jahohi da suka fito daga shiyyoyi shida na ƙasar nan, inda ta samu lambobin yabo masu daraja har uku.

Hukumar Kula da Taswira da Zamanantar da Harkokin Filaye ta Gombe (GOGIS) ta lashe lambar yabo ta hukuma “Mafi Fice a Kula da Taswira da Zamanantar da Harkokin Filaye” yayinda aka karrama Babban Daraktanta Dr. Kabiru Usman Hassan da lambar yabo ta “Distinguished GovTech Trailblazer’s Award” saboda irin gudunmawar daya bayar a wannan fanni.

Hukumar Tabbatar Da Bin Ƙa’idoji da Tsare-Tsare ta Jihar Gombe (Due Process Office) kuma ta samu lambar yabo ta “Hukuma Mafi Fice a Fagen Ƙirƙiro Sabin Harkoki na Zamani. Haka kuma an karrama Babban Daraktan Hukumar, Babayola Mohammed Isa da lambar yabo ta “Distinguished GovTech Trailblazers’ Award” saboda kyakkyawan jagorancin da ya nuna wajen ciyar da harkokin fasaha na gwamnati (GovTech) gaba, tare da gudanar da harkokin mulki na zamani a ma’aikatun gwamnati.

Bugu da ƙari Jihar ta Gombe ta sake samun lambar yabo, inda aka baiwa Jami’ar Jihar Gombe (GSU) lambar yabo ta “Jami’ar Jiha Mafi Fice a Harkokin Yanar Gizo”, wadda hakan wata shaida ce ta jajircewar jami’ar wajen inganta fasahar zamani.

An karrama Mataimakin Shugaban Jami’ar Farfesa Aliyu Usman El-Nafaty da lambar yabo ta “Distinguished Trailblazer’s Award” saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci bunƙasa tsarin tafiyar da mulki na zamani a fannin ilimi.

Da yake jawabi a wajen taron, Babban Daraktan Ofishin Sake Fasalta Aikin Gwamnati, Dr Dasuki Ibrahim Arabi, ya yabawa gwamnatin Jihar Gombe bisa manyan nasarorin data samu a fagen fasaha, inda ya yaba mata a matsayin ɗaya daga cikin jihohin dake ci gaba a harkokin tattalin arzikin zamani cikin sauri a Najeriya.

Yace karramawar da aka yi wa Gombe wata alama ce ta jajircewarta wajen ciyar da harkokin fasaha na gwamnati (GovTech) gaba, da gudanar da harkokin mulki na zamani ta hanyar fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire.

Dr Arabi yace babu hukumar data san cewa ana bibiya da nazartarta kafin wannar karramawa, yana mai cewa hakan ya biyo bayan zaɓen fidda gwani ne da aka yi a faɗin ƙasar nan da kuma tsarin kaɗa ƙuri’a ta yanar gizo da ake yi ta gidajen rediyo da talabijin da jaridu.

Yace an ɓullo da tsarin ne don karramawa da zaburar da hukumomi da ɗaiɗaikun jama’a dake samar da mafita, tsare-tsare da shirye-shirye ta hanyar amfani da fasaha wajen inganta ayyukan gwamnati da gudanar da harkoki na zamani.

A jawabansu daban-daban bayan karɓar kyaututtukan, Dr Kabiru Usman Hassan da Babayola Mohammed Isa, sun godewa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, bisa gagarumin goyon bayan da yake ba su da hukumominsu da kuma yadda gwamnatinsa take maida hankali a harkar mulki da tattalin arziki.

Taron ya samu halartar Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume wanda ya samu wakilcin Babban Sakatare mai ritaya a Gwamnatin Tarayya, Dr. Ibrahim Jalo Daudu, da Babban Daraktan Hukumar NASREA Farfesa Aliyu Jauro, wani fitaccen ɗan Jihar Gombe wadda shi ma ya samu lambar yabo a wajen bikin, da dai sauran manyan baki.

 

Daga Fatima Abubakar.