Wike ya ki amincewa da bukatar hukumar kwastam ta Najeriya na kwato fili da aka kwace a FCT.

0
19

Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi watsi da bukatar hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) na sake duba filayen da hukumar ta FCT ta kwace.

Ministan ya sanar da hakan ne a lokacin da jami’an kwastam karkashin jagorancin mukaddashin Kwanturola Janar Adewale Adeniyi suka kai masa ziyara a Abuja ranar Alhamis.

Tozali ta rawaito cewa hukumar ta NCS na cikin hukumomi da kungiyoyi da kuma daidaikun mutanen da FCTA ta kwace filayensu saboda gazawar su na bunkasa filayensu.

Adeniyi ya bukaci fili don gina makarantun firamare da sakandare ga yaran jami’an kwastam sama da 2,000 da ke zaune a babban birnin tarayya Abuja.

“A cewan Ministan, ya karanta wasiƙar ta Kwastam a kan filin  da aka soke, b amma ba abinda  zan iya yi.
Ya ce FCTA za ta tallafa wa wannan hidimar na gina wa ‘yayan jami’an ta makarantun firamare da sakandare  domin cimma manufofin ta amma ya koka da yadda aka bai wa hukumomin gwamnati filaye a babban birnin tarayya Abuja aka ki bunkasa su.

Dangane da filin ci gaban makarantu, ministan ya tabbatar wa shugaban kwastan cewa za a yi la’akari da shi amma da sharadin hukumar za ta yi alkawarin bunkasa filin a cikin wani kayyadadden lokaci amma idan aka ki bin
umarnin ministan ya ce za a kwace filin.“Makaranta, masu mahimmanci. Ba ‘ya’yan jami’an kwastam ne kadai za su halarci makarantun ba.
“Manufana a yanzu ita ce, kafin mu ba kowace hukuma fili, sai ta kuduri aniyar cewa za ta bunkasa kasar nan da wasu shekaru , kuma idan ba a bunkasa ba, ya kamata FCT ta karbe filin.

“Ku tabbata cewa zan amince da filin makarantar. Ka kawo aikace-aikacen; Zan sa hannu kuma in ba wa darektan filayen ya ba da filin da za ku iya amfani da shi,” in ji Wike.

Tun da farko, shugaban kwastan ya ce ya kai ziyarar ne domin taya Wike murnar nadin da aka yi masa a matsayin Ministan babban birnin tarayya Abuja da kuma ayyukan da ya yi a yanzu.

Ya bayyana hidimar kwastam a matsayin mai ruwa da tsaki a babban birnin tarayya Abuja tare da jami’ai sama da 2,000 da ke zaune a babban birnin tarayya Abuja da kuma bayar da gudunmawar ci gaban birnin.

Sai dai ya ce ba dukkan ‘ya’yan jami’an ne za su iya shiga makarantun gwamnati ba, yana mai jaddada bukatar samar da ingantaccen ilimi ga ‘ya’yansu.

Don haka ya bukaci a ba ‘ya’yan jami’an makarantar firamare da sakandire fili.

 

Daga Fatima Abubakar.