Gwamna Inuwa Ya Naɗa Ibrahim Isa A Matsayin Shugaban Kafar Yaɗa Labarai Ta Jahar Gombe

0
20

Gwamna Inuwa Ya Naɗa Ibrahim Isa A Matsayin Shugaban Kafar Yaɗa Labarai Ta Jahar Gomb

… Kana Ya Ɗaga Darajar Dr. Ishiyaku Babayo Daga Babban Mataimaki Na Musamman (SSA) Zuwa Mai Ba Da Shawara Na Musamman Kan Abokan Hulɗan Ci Gaba

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya amince da naɗin Ibrahim Isa na Gidan Rediyon BBC a matsayin Babban Daraktan Kafar Yaɗa Labarai ta Jihar Gombe (GMC).

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi, ne ya sanar da amincewar gwamnan, yana mai cewa naɗin na Ibrahim Isa, wadda ya fara aiki nan take, ya samo asali ne daga nagartattun halaye da kwarewarsa a fannin yaɗa labarai.

Ibrahim Isa, yana da ƙwarewar aikin jarida ta fiye da shekaru ashirin, hakan yasa ya yi fice a matsayin ɗan jarida mai tura rahotanni, mai haɗa labaru da karanta su, kuma mai gudanar da shirye-shiryen talabijin kana manajan watsa labarai. Duba da gogewa da kwarewarsa, ana sa ran Ibrahim Isa zai yi amfani da sabbin dabaru da hikimomi a Hukumar Yaɗa Labarun ta Jihar Gombe don inganta harkokin yaɗa labarai.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana kwarin gwiwar cewa jagorancin Ibrahim Isa zai taimaka wajen bunƙasar ƙafar yaɗa labaran ta GMC da yi wa al’umma hidima ta hanyar samar musu sahihan labarai da suka dace.

Har ila yau, Gwamna Inuwa Yahayan ya amince da ɗaga darajar Dakta Ishiyaku Babayo Mohammed, daga matsayin babban mataimaki na musamman (SSA) kan haɗin gwiwa da abokan huldar ci gaba zuwa mai ba da shawara na musamman kan wannan fanni.

Sanarwar hakan wacce Sakataren Gwamnatin Jihar ya sanar, ta ce an ɗauki matakin ne duba da irin nasarorin da Dr. Mohammed ya cimma, da jajircewarsa na musamman da kuma tasirin da ya yi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci daga naɗa shi a matsayin mai bada shawarar.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana kwarin gwiwar cewa daga darajarsa zuwa muƙamin mai ba da shawara na musamman zai ƙara haɓaka shirye-shiryen haɗin-gwiwa na jihar tare da ƙara ƙaimi wajen samar da kuɗaɗe da tallafi daga ɓangarori daban-daban na ci gaba don ba da gudummawa ga jin dadi da ci gaban Jihar Gombe baki ɗaya.

Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe

 

 

 

 

Hafsat Ibrahim