Gwamna Inuwa Ya Samu Gagarumar Tarba Ta Ba Zata Biyo Bayan Nasarar Da Ya Yi A Kotun Ƙoli

0
4

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya samu tarba ta ba zato ba tsammani daga jiga-jigan Jam’iyyar APC, da ɗimbin masoya da magoya a lokacin da ya dawo Gombe bayan wata ziyarar aiki a wajen jihar da kuma nasarar da ya samu kwanan nan a Kotun Ƙoli.

Dandazon jama’ar da suka taru sun haɗa da ƴan kishin jam’iyya da magoya bayan APC, inda suka yi jerin gwano a garuruwan Nafaɗa da Funakaye da Kwami da kuma Gombe, don nuna jin daɗi da goyon bayansu ga Gwamnan, bayan nasarar shari’a da ya samu a Kotun Ƙoli.

Gwamna Inuwa Yahaya wanda yayi ta ƙoƙarin kaucewa duk wata gagarumar tarba, ya gaza shawo kan ɗimbin jama’ar da suke ɗoki da nuna farin cikinsu kan hukuncin da kotun ta yanke.

Gwamnan ya dawo ne daga Maiduguri inda ya jagoranci taron tunawa da Marigayi Sir Ahmadu Bello da ake yi duk shekara, kasancewarsa Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa.

Ya zaɓi dawowa Gombe ta hanya, amma sai dawowar ta zama wani shagali, inda magoya bayansa ƙarƙashin jagorancin jami’ai, da jiga-jigan jam’iyya, dama sarakuna suka yi masa maraba a hanyarsa ta dawowa, yayin da ya ratsa ta cikin ƙananan hukumominsu.

A Gombe, mataimakin gwamnan, Dr. Manassah Daniel Jatau ne ya jagoranci wassu manyan jami’an gwamnati wajen tarbar Gwamna Inuwa Yahaya a gidansa da kuma miƙa saƙon taya murna gare shi da Jam’iyyar APC bisa nasarar da suka samu a Kotun Ƙoli.

A duk wuraren da aka tsaya, an gudanar da addu’o’i na musamman domin Allah Ya ci gaba da yi wa gwamnan da gwamnatinsa jagora.

Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe