Kungiyar kasuwannin Dabbobi na cika Aljuhu da kudin Harajin Shanu a Kano

0
27

Kungiyar kasuwannin Dabbobi na cika Aljuhu da kudin Harajin Shanu a Kano

 

Shamsiyya Hamza Sulaiman

Jihar Kano na daya daga cikin cibiyar cinkaiya da aka juma ana damawa da su a arewacin Nageriya, duk da shahara tasu a fannin kasuwanci hakan bai sa gwamnatin jihar kallafawa makiyaya biyan kudin harajin shanu ba.

Amman da yawa daga cikin kasuwannin dabbobin jihar na kan gaba wajan karbar hajajin shanu a duk ranar da kasuwannin ke ci .

Kasuwar Dabbobi ta wudil na daya daga cikin misalan kasuwannin da ke karbar harajin shanu a kano, kasuwar na ci duk ranar juma’a, sannan akallah ana shigo da shanu kimanin dubu biyar a kowane sati, kungiyar yan kasuwar dabbobin na karbar harajin naira dari biyar kan kowace sah.

Uwa uba kungiyar yan kasuwan na kasafta kudin domin mikawa ofishin karamar hukuma naira dari biyu, daga bisani hukumar kasuwa ta soke canjin naira dari uku a Lalitar ta.

lamarin haraji dai ya zama ruwan dare a fadin Nageriya, domin kuwa haka abin yake a daukacin kasuwannin dabbobin jihar ta kano kamar yanda Tozali Tv ta kai ziyarar gani da ido karamar hukumar Wudil,Kura, Bichi,da Danbatta domin ganin irin wainar da ake toyawa ka sha’anin harajin dabbobin.

Kasuwar Dabbobi ta wudil na tara akallah naira miliyan 2.5 a kowane mako,sannan naira miliyan 10 a kowane karshen wata, haka zalika naira miliyan 120 a duk karshen shekara.

Babban abin dubawar shine naira dari biyu kacal aka zana a jikin takardar shaidar biyan harajin, da kuma sahalewar shugaban karamar hukuma.

Hakan take a karamar hukumar Kura, Bichi da Danbatta duk da cewa basu kai kasuwar wudil cika da tumbatsa a fannin hada hadar shanun ba,kasan cewar ta shakun dum.

Alhaji Umaru Adamu Sarkin fulanin giware daga karamar hukumar Dan batta, yace suna fuskantar karancin muhalli da kuma rashin waddatacen abincin da zasu ciyar da shanu, mussaman korama, rafi ku kuddidifi wajan shayar da shanu nasu, ga kuma tsadar rayuwa da ake fama da ita.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunnanta tayi karin haske da cewa akan basu kiwo shawanu tsawan shekaru ba tare da la’akari da halin matsin rayuwa ba, ba’a biyan su ladan aikin su, Fulani da dama sun zama tamkar bayi a sakamakon karbar amanan shanun alhazan birini,duk da wannan kalubalan hakan ba ya hana mai dabba mika mua gaban kuliya ida an samu akasi ko kuskure a duk sanda ya waiwaye shanun sa.

Alhaji kwai_kwai na daga cikin jagororin kungiyar miyate Allah reshen jihar kano karamar hukumar Bichi ya koka matuka kan yanayin da Fulani da makiyaya ke ciki a fadin jihar, sannan ya ce kungiyar su a shiye take wajan dawo da martabar kiwo da kuma kawo shulu da daidaito tsakanin Fulani, makiyaya dama alumar gari,

Alhaji Garba Bichi shine dagacin garin Bichi yace a baya an karbi harajin shanu a kano kimanin shekaru 60 baya amman a yanzu babu wannan dokar kasancewar chanjin da banbancin ra’ayin siyasa.

Abdulmuminu Anjumawa baban daractor ma’aikatar harajin reshen jihar kano yace haraji abune mai matukar mahimmaci wajan farfado da tattalin arzikin, aman babu wata doka a hukumance dake karbar haraji makiyaya a jihar kano, kuma koda za’a kirkirota to ya zama wajibi a fara tallafawa makiyayan da Abubuwan more rayuwa.

Comishinan yada labarai Baba Halilu dan Tiye yace gwamnatin kano ba ta da masaniya kan batun karbar harajin shanu a kasuwani dabbobi a fadin jihar, sannan babu wata doka da ta yi nuni da hakan

Munyi kokarin jin ta bakin Shugabar karamar hukumar Wudil Hajiya Bilkisu Indabo Amman ta ki cewa komai kan batun.

Mun kuma wai waye Shugaban kasuwar Dabbobi ta wudil Alhaji Dan Titi, domin ji daga bakin sa, shima lamarin ya ci tura.

Matashi Kabiru Abubakar kabiru jigo ne a kasuwar dabbobin ta wudil ya fadi dalilin karbar harajin, inda yace suna bukasa kasuwar ta fanin biya masu zubar da shara, kula da sha’anin tsaro da dai sauransu, duk da cewar basa samun kulawa daga gwamnatin ta kano.

Sai kuma Alhaji Ado Muhammad Shugaban karamar hukumar Danbatta ya tabatar da cewar hukumar kasuwar na aika musu naira dari biyu duk sati kan kowane sah, ya kuma musanta naira dari ukun da kungiyar kasuwar ke karawa a kai.

Shugaban karamar hukumar Kura Yahya Tijjani Kura ya ce bashi da masaniya kan batun biyan harajin shanu a kura, hasali ma bai san wata kasuwar shanu a karamar hukumar ta sa ba.

Mallam Bala kura shima jigone a kasuwar dabbobin ya kuma bayyana alfanun karbar harajin dabbobin wajan bunkasa sha’anin tsaro da Tsaftar kasuwar.

A nasa bangaran Shugaban karamar hukumar Bichi shima ya musanta batun cin kasuwar dabbobin a yakin nasa, sakamakon sauyin muhali da gwamnatin kano tayi musu, inda yace nan bada jumawa ba kasuwar zata dawo da hada hadar shanun kamar yanda aka santa a baya.

Duk da cewar min samu zantawa da kabiru Abubakar Shugaban kasuwar dabbobin ta bichi ya ce a yanzu haka babu waddatacen shanu a kasuwar dabbobin sakamakon sauyin muhali da gwamnatin kano tayi musu a halin yanzu, Amman duk da haka akan karbi harajin a hukumance a cewar sa.

Makiyaya da dama a jihar da cigaba da kokawa kan koma bayan da fannin kiwo ke samu, wanda suke gannin hakan a matsayin nakasu ga tattalin arzikin arewacin Nageriya.

Hafsat Ibrahim