Da dumi-dumi-Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa hukumar kula da ma’aikata a Abuja, wato Civil Service Commission;In ji Wike.

0
27

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya janye hukumar babban birnin tarayya, FCTA, daga asusun bai daya, wato Treasury Single Account, TSA, inda ya share hanya mai kyau ga FCTA karkashin jagorancin Nyesom Wike, ta yi amfani da IGR na kudaden shiga na cikin gida domin bunkasa babban birnin kasar nan.

A wani taron manema labarai  da ministan ya yi a yau Juma’a a Abuja, Wike ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ya amince da kafa hukumar kula da ma’aikata ta babban birnin tarayya Abuja wato Civil service commission, da kuma sakatariyar kula da ayyukan mata,wato mandate Secretary of women affairs na babban birnin tarayya domin baiwa ma’aikata da mata damar ci gaba a kowane bangare na sana’ar su da rayuwa baki daya.

Zaku samu cikakken bayanai daga baya.

 

Daga Fatima Abubakar.