Gwamna Inuwa Yahaya Ya Cika Da Alhini, Yayin Da Maidalan Gombe Ya Rasa Yaya 6 Sanadiyyar Hatsarin Mota

0
22

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Cika Da Alhini, Yayin Da Maidalan Gombe Ya Rasa tare da Yaya 6 Sanadiyyar Hatsarin Mota

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga Maidalan Gombe, bisa rasuwar iyalan gidansa 6 a wani mummunan hatsarin mota a kan hanyar Azare zuwa Gombe jiya Lahadi.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Ismaila Uba Misilli ya fitar tare da miƙa ta ga gidan talabijin da mujallar tozarta yau Litinin.

Gwamna Inuwa wanda ya halarci Sallar Jana’izar mamatan tare da Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Dr Abubakar Shehu Abubakar na 3 da sauran ɗaruruwan jama’a, yace rashin iyalai a irin wannan mummunan yanayi abu ne mai matuƙar tayar da hankali.

Yace wannan abin baƙin cikin ya shafi ɗokacin al’ummar Gombe baki ɗaya.

Yace “Muna miƙa ta’aziyyarmu ga Maidalan Gombe da ɗokacin iyalansa a wannan mawuyacin lokaci. Rasuwar mutum 6 ‘yan gida guda a irin wannan mummunan hatsarin mota ba kawai babban rashi ne ga iyalanka ba, ya ma shafi ɗokacin al’ummar Gombe baki ɗaya”.

“Kalmomi ba za su iya bayyana irin jimami da takaicin da kuke ciki ba sanadiyyar wannan gagarumin abin baƙin cikin daya sameku ku da masoyanku. Ku sani cewa muna tare da ku a cikin wannan hali a addu’o’inmu yayin da kuke cikin wannan hali mai raɗaɗi da takaici”.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayan ya gafarta musu kurakuransa, ya saka musu da Aljannar Firdausi.

Amin

 

 

 

 

Hafsat Ibrahim