NDLEA ta lalata haramtattun kwayoyi sama da dubu 30 da aka kama a Legas da Ogun.

0
27

 

Hukumar NDLEA ta lalata haramtattun kwayoyi sama da dubu 30 da aka kama a Legas da Ogun.

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, a ranar yau Talata 16 ga Afrilu, 2024, ta tabbatar da lalata haramtattun kwayoyi masu nauyin Kilogram 304,436, daidai da lita 40,042 kenan da aka kama a sassan jihohin Legas da Ogun.

Da yake jawabi a wani takaitaccen biki da gudanar na lalata miyagun kwayoyyin da akayi a bainar jama’a a Badagry na jihar Legas, Shugaban Hukumar Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya ce lalata haramtattun kwayoyi da aka kama ya biyo bayan umarnin da kotu ta basu ne, kamar yadda suka bukata.

Yace sunyi hakan ne domin samun karin goyon bayan jama’a kan kokarin da hukumar NDLEA da sauran masu ruwa da tsaki ke ci gaba da yi na dakile matsalar shan muggan kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Ya kuma mika godiyarsa ga sarakunan gargajiya, shugabannin hukumomin tsaro, malamai, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma sauran masu ruwa da tsaki da suka shaida bikin.

Yayin da yake tabbatar da cewa NDLEA ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na kawo karshen matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a kasar, Marwa ya yi kira da a kara tallafawa al’umma kan ayyukan Hukumar.

Ya kuma yi kira ga ƴan Nijeriya da su kasance masu taimakawa wajen yaƙin da Hukumar take yi da Muggan Kwayoyi (WADA) domin tsaftace al’ummomi.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu wanda ya samu wakilcin shugaban karamar hukumar Badagry ta Yamma, Olusegun Onilude ya bayyana jin dadinsa da kokarin da hukumar NDLEA take yi na shawo kan matsalar shan miyagun kwayoyi a kasar nan.

 

 

Daga : Shamsiyya Hamza Sulaiman