Gwamna Jihar Gombe ya ziyarci ministan kasafin kudi da tsare- tsare na Gwamnatin Tarayya

0
18

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Ziyarci Ministan Kasafin Kudi Da Tsare- Tsare na Ƙasa Don Ƙarfafa Alaƙa Tsakanin Jihar Gombe Da Gwamnatin Tarayya .

 

Daga Gombe

Yunusa Isah kumo

A jiya Alhamis ce Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya ziyarci mai girma Ministan Kasafin Kudi Da Tsare-Tsare Sanata Abubakar Atiku Bagudu, a ofishinsa dake Abuja.

 

Shugabannin biyu sun yi ganawar ce a asirce, inda suka tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi muradun Jihar Gombe da kuma manyan tsare-tsaren ƙasa da nufin samar da haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Gombe da Gwamnatin Tarayya don tinkarar wassu manyan ƙalubale da kuma inganta ayyukan raya ƙasa.

 

A yayin da Gwamna Inuwa Yahaya ke ci gaba da dabbaka muradun Jihar Gombe a matakin ƙasa baki daya, irin wannan ganawa da manyan masu ruwa da tsaki na gwamnatin tarayya tana nuna irin himmatuwarsa na zaƙulo duk wassu damammaki daga gwamnatin tarayya don amfanin al’ummar Gombe.

 

Daga karshe  Gwamnan ya samu rakiyar Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai kuma ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Akko, Rt. Hon. Usman Bello Kumo.

 

Ismaila Uba Misilli

Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe.

 

 

 

 

 

Hafsat Ibrahim