Rahotanni sun bayyana cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya rufe akalla kwalejojin fasahar kiwon lafiya masu zaman kansu guda ashirin da shida a jihar.
Gwamnati ta ce manyan cibiyoyin na gudanar da ayyukansu ba bisa ka’ida ba, don haka suna da illa ga lafiyar jama’a, ci gaban ilimi da ingantaccen tsarin kiwon lafiya gaba daya a jihar.
Da take sanar da rufe makarantun a cikin wata sanarwa da ta bawa maneman labarai a ranar Juma’a, ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta bakin jami’ar hulda da jama’a ta jihar, Hadiza Namadi ta ce wasu daga cikin kwalejojin na karbar makudan kudade daga iyaye ta hanyar ‘ya’yansu.
Namadi ta ce: “Ma’aikatar ta lura da tsananin damuwa, ci gaba da yaɗuwar Cibiyoyin Horar da Kiwon Lafiyar Jama’a (PHTIs) ba bisa ƙa’ida ba a cikin Jiha ba tare da bin wasu ƙa’idojin da suka shafi kafa da gudanar da irin waɗannan makarantu kamar yadda hukumomin gudanarwa da sauran hukumomin da abin ya shafa suka ayyana.
Abin takaici ne sosai a fahimci cewa wasu daga cikin cibiyoyin da ba a san su ba ba su da takamaiman shafuka kuma suna ba da shirye-shirye masu ban sha’awa game da tsarin karatun da aka kafa, tare da karbar makudan kudade ga ɗalibai da iyayensu.
“Saboda haka, ana sanar da jama’a game da rufe dukkanin cibiyoyin horar da lafiya ba bisa ka’ida ba (HTIs) a cikin jihar nan take, har sai an kammala binciken da ya dace.”
Ga makarantun da abin ya shafa Kamar haka:
- Unity College of Health Science & Technology Dorayi Karama (K.G/Mai), Gwale LGA Danbatta LGA
- Khalil College of Health Science & Technology Zaria Road, Opp Gadar Lado Darmanawa Unguwa Uku Opp. Hisbah Office, Karkasara, Opp. Bilal Mosque, Tarauni LGA; Danbatta LGA; Wudil LGA
- Shamila College of Health Science & Technology Gezawa LGA
- Autan Bawo College of Health Science & Technology Rano LGA
- Trustee College of Health Science & Technology Jakara, Dala LGA – Kano Bachirawa, Ungoggo LGA – Kano
- Eagle College of Health Science & Technology, Bichi LGA
- Albakari College of Health Science & Technology, Rijiyar Zaki, Ungoggo LGA – Kano
- Jamatu College of Health Science & Technology, Kura LGA
- Savanna College of Health Science & Technology, Wudil LGA
- Institute of Health Education – Ahmadiyya, Opp. INEC Office
- Jamilu Chiroma College of Health Science & Technology – Kings-Garden, Zungeru road, Opp. Airport Road, S/Gari’
- Sir Sanusi College of Health Science & Technology Matan Fada Road
- Aminu Ado Bayero College of Health Science & Technology
Ado Bayero Layout, Dandinshe Yamma – Dala LGA - Awwab College of Health Science & Technology, Salanta, Gwale LGA
- Gwarzo Unity College of Health Science & Technology, Gwarzo LGA
- Al-wasa’u College of Health Science & Technology, T/Fulani, Nassarawa LGA – Kano
- Kanima Academy, Layin Dan-kargo, Zangon Dakata, Nassarawa LGA – Kano
- Muslim College of Health Science & Technology, Zungeru Road, Fagge LGA – Kano
- Utopia College of Health Science & Technology, Jigirya JSS, Yankaba, Nassarawa LGA – Kano
- Jama’a College of Health Science & Technology, Na’ibawa Yan-lemo, Tarauni LGA – Kano
- Kausar Healthcare Academy, Jos Road, Beside Islamic Centre, T/Wada LGA – Kano
- Shanono College of Health Science & Technology, No. 33 Kofar Gari, Shanono LGA – Kano
- Institute of Basic Health Education, Jakara Garden, Airport Road, Nassarawa LGA – Kano
- School of Health Technology, Habib Faruq Girls Sec. Sch., Gidan Kara, Kurna T/Fulani
- School of Health Technology, Bachirawa Special Primary School, Ungoggo LGA
- Fudiyya School of Health Sciences, Danrimi, ‘Yan-babura Rijiyar Lemo, Fagge LGA. By:Firdausi Musa Dantsoho