NYU ta roki Tinubu da kada ya siyasantar da yajin aikin ASUU

0
17

Kungiyar matasan Najeriya (NYU) ta yiwa Asiwaju Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, aniyar sa na shiga tsakani a yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dade tana yi.

Tinubu, a wata ganawa da ya yi da shugabannin kungiyar dalibai ta kasa (NANS) a Osogbo, ya ce: “Ina tabbatar muku, ba za mu yi amfani da kofar baya ba, domin shi ma shugabanmu Buhari ya nuna kokensa.  a cikin sa’o’i 48 da suka gabata kuma sakamakon hakan ya bar mana kofar shiga tsakani.

Da yake mayar da martani ga kalaman Tinubu a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar NYU Comrade Chinonso Obasi ya fitar, ya ce: “Abin takaici ne da bacin rai gare mu, kungiyar matasan Najeriya muka samu wannan alkawarin cin fuska daga wani r siyasa kamar Bola Tinubu.

“An fadakar da mu, mu yarda cewa gwamnatin APC tana yin wasan siyasa ne da rayuwan  matasan Najeriya ta hanyar hana su zuwa makaranta tsawon watanni biyar da suka gabata, don ta yi amfani da yajin aikin a matsayin wata budaddiyar hanya ga ‘yan siyasarta na Jagaban don samun wasu fa’idojin zabe. 

By: Firdausi Musa Dantsoho