Hukumar babban birnin tarayya ta bayyana kudirinta na ganin an samar da ingantaccen ilimi a kasar nan.

0
12

Sakataren ilimi na babban birnin tarayya Abuja, Dokta Danlami Hayyo, ya bayyana hakan, a lokacin da yake kaddamar da littafin kulab din jinsi na makarantun babban birnin tarayya.

Sakataren ya umurci shuwagabannin makarantun Sakandare dake FCT da su mallaki kungiyoyin jinsi a makarantunsu daban-daban.

Hayyo ya bukaci shugabannin makarantun su tabbatar da dacewa da jinsi, aminci da ingantaccen yanayin makaranta wanda ya dace da ingantaccen ilimi.

A cewarsa, sakatariyar ilimi ta FCT ce ta samar da littafin Manual Club na FCT a wajen taron tuntubar juna na yini kan bunkasa kungiyoyin jinsi a makarantu domin kara bunkasa shi.

Sakataren ya bayyana cewa kungiyoyin jinsi na iya taka muhimmiyar rawa wajen tsara tsarin kawar da duk wani nau’i na GVB a Najeriya; yana bayyana cewa batutuwan GBV suna da matuƙar damuwa duk saboda mugun

Kalamansa: “Yawancin yaran makaranta na maza da mata ba a hana su ilimin asali da kuma dabarun da suka dace don ba su damar gudanar da rayuwa mai aminci da inganci”.

“Saboda haka, yana da mahimmanci ga FCTA ta samar da kungiyoyin kula da jinsi a duk makarantun da ke cikin FCT a matsayin hanyar da za ta bi wajen warware gibin jinsi a cikin ilimi da kuma amfani da cikakkiyar damar ‘yan mata da maza,” in ji shi.

Sakataren ya kara da cewa, “an samar da littafin ne a matsayin jagorar gudanarwa ga kungiyoyin jinsi a dukkan makarantun FCT.”

Shi ma a nasa jawabin, Daraktan Admin da Kudi, Alhaji Abdulrazaq Leramoh, ya bukaci shugabannin makarantu da shugabannin malamai da su mallaki kungiyoyin jinsi; tare da jaddada muhimmancinsa a matsayin hanyar magance tashe-tashen hankula, ba wai a makarantu kadai ba har ma a cikin al’umma.

 

Daga Fatima Abubakar.