Hukumar ICPC ta sake kama tsohon magatakardar JAMB Dibu Ojerinde

0
45

 

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) sun sake kama Dibu Ojerinde, tsohuwar magatakardar hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB.

Hakan na zuwa ne bayan Jimoh Olabisi, tsohon mataimakin darakta a JAMB kuma shaidan ICPC, a gaban kotu a ranar Laraba, 25 ga watan Janairu, ya ce Ojerinde ya yi amfani da shi wajen karkatar da kudaden gwamnatin tarayya.

 An gurfanar da tsohon magatakardan wanda aka zarge shi da aikata zamba da yawa a lokacin da yake shugabantar Hukumar JAMB da Hukumar Jarrabawa ta Kasa (NECO), a ranar 6 ga Yuli, 2021, kan tuhume-tuhume 18 da suka hada da karkatar da kudade har N5.2  biliyan.

 

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa Ojerinde wanda ya musanta zargin da ake masa kuma aka bayar da belinsa a kan kudi Naira miliyan 200, jami’an ICPC ne suka kama shi a Abuja a ranar Alhamis, 26 ga watan Janairu a harabar wata babbar kotun tarayya.

 

Daga:Firdausi Musa Dantsoho