Hukumar NALDA ta ba da tabbacin cewa kasar ba zata fuskanci karancin abinci ba a shekarar 2023

0
3

Hukumar bunkasa filayen noma ta kasa NALDA ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa kasar ba za ta fuskanci matsalar karancin abinci ba a shekara mai zuwa, duk kuwa da irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi a filayen noma a manyan wuraren amfanin gona a kasar.Hukumar ta ce, hukumar tana dasa hekta 500 na alkama na noman rani a jihohin Adamawa, Yobe, Jigawa, Gombe da kuma Taraba domin habaka samar da abinci.Sakataren zartarwa na hukumar, Prince Paul Ikonne, wanda ya kawar da batun karancin abinci a shekara mai zuwa, ya ce ta samu injuna da kayan aiki don hanzarta noma a yankuna shida.Ikonne ya bayyana haka ne a yayin wani taron manema labarai jiya a Abuja inda ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya tsaf domin baje kolin nasarorin da NALDA ta samu cikin shekaru biyu, a Abuja.A cewarsa, an samu gagarumin ci gaba wajen tasiri ga matasa manoma da mata ta hanyar ayyukan noma da dama.Ya kara da cewa shugaban kasar ya aza harsashi mai karfi domin hukumar ta yi aiki yadda ya kamata tare da manoma sama da 50,000 ban da matan da ya zuwa yanzu suka ci gajiyar amfanin gona da kiwo.Ya ce, “NALDA ta cika da farin ciki a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo da ita da nufin karfafa gwiwar matasan Najeriya da su rungumi harkar noma, da magance matsalar samar da filaye, da samar da filaye.“A yanzu haka, muna samar da hekta 500 na noman alkama a wannan noman rani kuma tun daga wannan lokacin har zuwa yau, NALDA na ci gaba da yin tasiri mai kyau a rayuwar ‘yan Najeriya.

Daga:Firdausi Musa Dantsoho