Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta samu tambayoyi da dama dangane da shawarwarin tsaro da ofishin jakadancin Amurka dake Abuja ya bayar a jiya 23/10/22. Jama’a na iya tunawa cewa Sabis ɗin na ba da irin wannan gargaɗi daban-daban a lokuta-lokuta a baya.
Yayin da yake ba da shawarar cewa kowa da kowa ya ɗauki matakan da suka dace, an umurci jama’a da su kasance cikin faɗakarwa tare da taimakawa hukumomin tsaro da bayanai masu amfani game da barazana da ayyukan masu aikata laifuka da ake zargi da ke kewaye da Abuja.
A halin da ake ciki, Hukumar ta yi kira da a kwantar da hankali yayin da take aiki tare da sauran hukumomin tabbatar da doka da masu ruwa da tsaki don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ciki da wajen Abuja.
Wannan rahoton dai ya zo ne daga jami’in hulda da jama’a na sashen Sabis na hedikwatar kasa a Abuja Mr. Peter Afunanya.
Daga Fatima Abubakar.