MAN ALAYDI DA ANFANIN SA.

0
920

MAN ALAYYADi

Man alayyadi, ana samu sa ne daga kwallon man ja. Wato idan an bare wannan fatar da ake yin man ja da shi. Sai a fasa kwallon, akwai wata kwakwa a ciki. to wannan kwakwar a jikin ta ake samun man alayyadi.

Amfani man alayyadi.

1= Man alayyadi Yana da faaidodi da anfani Mai tarin yawa ga Dan adam.

2=Cin abince tare da man alayyadi Yana rage hadarin kamuwa da ciwon zuciya.

3=Idan aka hada man alayyadi tare da man kwakwa ana shafawa, yana sa fata laushi da sheqi.

4=Mai Fama da ciwon daji na Fata Sai ya hada man alayyadi da Garin habbatusauda ya dinga Shafawa zai warke da wuri.

5=Mai lalular shanyewar barin jiki. Sai a dinga baiwa mara lafiya man alayyadi cokalin daya a cikin ruwan dumi yana sha Kuma adinga shafa masa a jikin shi.

6=Shan man alayyadi Yana karfafa garkuwan jiki,da lalular ciwon ciki in Kasha alayyadi Yana maganin sa.

Daga Zainab Sani Suleiman.