Ko a jiki na game da sake dawo da binciken bidiyon dala:In ji Ganduje.

0
34

Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ko a jikinsa, game da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na ci gaba da binciken bidiyon dala, wanda ake zargin an nuna shi yana karbar rashawa.

Ita dai gwamnatin Kano a ta bakin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Muhuyi Magaji Rimin Gado wanda aka mayar kan kujerarshi bayan gwamnatin Kanon ta tube shi, za a dawo da binciken da aka fara tun lokacin da bidiyon ya bulla.

Ya ce baya ga bidiyon dala ma, akwai wasu zarge-zargen da ake yi wa gwamnatin ta Ganduje da ta gabata na yin wadaka da baitulmalin jihar musamman kudaden kananan hukumomi, da maganar kwangiloli da kudaden haraji.

Sai dai tsohon kwamishinan watsa labaran jihar Muhammad Garba, wanda na hannun daman tsohon gwamnan Kanon Abdullahi Ganduje ne, ya ce wannan abu ba ya daga masu hankali ko kadan.

A cewar Malam Muhammadu Garba ”Magana ce ta kotu,kuma shi Muhuyi a matsayinsa na lauya ya fi kowa sanin me ya kamata ya yi, mun zuba ido mu ga abun da za su yi, idan yana da dama ya binciki maganar da ke kotu ya fi kowa sani, idan ma ba shi da dama ya fi kowa sani”.

Ya kara da cewa ”ko da na yi magana da gwamnan Ganduje abun bai dame shi ba, saboda haka wannan lamari ne na shari’a.

Ya ce idan ta kama tsohon gwamnan ya je idan an gayyace shi zai nemi shawarar lauyoyi kan abun da ya kamata ya yi.

A baya-bayan nan ne dai tsohon gwamnan Kanon ya nemi kotu, ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC daga duk wani bincike a kan lamarin bidiyon dalar, bisa hujjar cewa hukumar ba ta da damar gudanar da bincike kan lamarin.

A shekarar 2019 ne wata jarida a Najeriyar ta wallafa wani bidiyo da take zargin na Ganduje ne, ana mika masa kudi yana karba.

Yayin wata hira da BBC daga bisani, gwamna Gandujen da bakinsa ya ce wannan bidiyon ba gaskiya ba ne, hada shi aka yi, inda ya lashi takobin daukar mataki kan lamarin.

A cewarsa ”wannan bidiyo da aka fitar ba gaskiya ba ne, kuma ana bincike a kai, za a dauki mataki kan duk wanda ke da hannu”

Ya ce wadanda suka yi bidiyon sun yi ne a matsayin maƙarƙashiya domin hana shi shiga zaɓen 2019, sai dai ba su ci nasara ba.

Daga Fatima Abubakar.