Kotu Ta Ba da belin Emefiele akan N20m

0
14

An bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kan kudi naira miliyan 20.

Sharadin belin ya hada da gabatar da wanda zai tsaya masa kadarori da ke da hurumin kotun da ke Ikoyi a Legas, ajiye fasfo dinsa da kuma samar da ma’aikacin gwamnati da bai gaza mataki na 16 ba don cikakken beli.

An gurfanar da Emefiele a gaban mai shari’a Nicholas Oweibo da ke zama a babbar kotun tarayya da ke Legas a ranar Talata.

Masu gabatar da kara sun zargi Emefiele da samun bindigar ganga guda (JOJEFF MAGNUM 8371) ba bisa ka’ida ba.

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da shi a gaban kotu cikin tsatsauran matakan tsaro.

An kuma tuhume shi da laifin mallakar bindigogi da alburusai ba bisa ka’ida ba.

A cewar gwamnati, laifin ya saba wa Sashe na 4 na Dokar Makamashi, Dokokin Cap F28 na Tarayya 2004, kuma an hukunta shi a karkashin Sashe na 27 (1b) na wannan Dokar.

Firdausi Musa Dantsoho