Tsohon dan wasan Super Eagles Tijjani Babangida ya tsira daga hatsarin mota, inda ya rasa dan uwansa.

0
40

Innanulillahi wa inna laihi rajiun

Tsohon dan wasan Super Eagles Tijjani Babangida ya tsira daga hatsarin mota, inda ya rasa dan uwansa.

 

Allah yayiwa Dan uwa tsohon dan wasan Najeriya Ibrahim babangida rasuwa, a hanyarsa ta Zaria sakamakon Hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Lamarin ya faru ne a Yammacin ranar Alhamis  inda Hatsarin ya ritsa da su. A yanzu haka ma  Tijjani Babangida da Iyalansa suna cikin mawuyacin hali yayin da likitoci ke  gwagwarmaya don ceto rayuwarsa.

Tijjani Babangida Ya Rasa Ɗan uwansa Yayin da Matarsa Maryam Waziri da dansu Ke cikin wani Yanayi.

TSOHUWAR JARUMA LAILAH DA MIJIN NA TA SUN SAMI HATSARI NE AKAN HANYAR SU WANDA AL’AMARIN YA KAI GA RASA DAN UWAN MIJI.

Wannan na zuwa ne bayan mummunan hatsarin mota da ya afku dasu .Da Kuma kaninsa.

Sanadin hatsarin motar ya jawo rasa kanin mijinta mai suna Ibrahim Babangida nan take wanda tuni aka yi sallar jana’izarsa. Bayan faruwar hatsarin, an kwashi Maryam da kuma mijinta, Tijjani Babangida zuwa asibiti domin ba su kulawa na musamman. Bayan shafe kwanaki biyu a asibitin ne aka sanar da ɗansu mai shekara daya ya rasu bayan samun munanan raunuka a hatsari.

 

Hafsat Ibrahim