Kotun ta chanja hukuncin da kotun fara sauraren ƙararrakin zabe a matakin jiha ta yanke ,kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana A.A. Sule a matsayin Wanda ya lashe zaɓen na jihar ta Nassarawa
.
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta ce gwamnan jihar Nasarawa A.A. Sule ne ya lashe zaɓen gwamnan da aka gudanar a jihar na watan Maris.
Alƙalan kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uchechukwu Onyemenam ne suka bayana haka yayin da suke yanke hukunci a shari’ar da ya shigar, dan gane da ƙalubalantar hukuncin kotun da abokin hamayyarsa David Ombugadu na jam’iyyar PDP .
A waccan shari’ar, kotun ta bawa ɗan takarar jam’iyyar ta PDP nasara, matakin da ya sa Gwamna Sule ya ɗaukaka ƙara.
Tun da sanyin safiyar Alhamis magoya bayan gwamnan suka taru a harabar Kotun Ɗaukaka Ƙarar dake birnin na Abuja domin jin yadda za ta kaya.
Rahotanni daga Lafia, babban birnin jihar na cewa ana zaman ɗar-ɗar tun da aka sanar da za a bayyana hukuncin na yau Alhamis.
Sai dai kotun ta Kore hukunci da karamar kotu ta Yi, inda ta Ayyana Dan takarar jam iyyar APC a matsayin Wanda yayi nasara
HAFSAT IBRAHIM