Kotun Koli Ta Kori Ƙarar da Jam’iyyar ADC Ta Shigar Kan Gwamna Inuwa Yahaya 

0
8

…Yayin Da Kotun Ta Ɗage Sauraron Ƙarar Da PDP Ta Shigar

Kotun Ƙoli ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da Jam’iyyar ADC da ɗan takaranta Nafiu Bala suka shigar kan nasarar da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya samu a zaɓen gwamna da aka yi ranar 18/03/2023, wanda kotun sauraren kararrakin zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka amince da shi tun farko.

ADC da Nafiu Bala sun ƙi amincewa da hukuncin kotunan game da sakamakon zaɓen, duk da cewa ƙuri’un da suka samu basu kai ko 2,000 ba a zaɓen.

Don haka kotun ta buƙaci sanin abin da jam’iyyar da ɗan takaranta ke nufi da ɗaukaka ƙarar. Ganin yanayin kotun, lauyoyin dake kare Nafiu Bala da Jam’iyyar ta ADC suka janye ƙarar da suka shigar, lamarin da ya sa kotun ƙolin ta yi watsi da ƙarar.

Idan dai za a iya tunawa, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Gwamna Inuwa Yahaya na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen, da ƙuri’u 342,821 daga cikin ƙuri’un da aka kaɗa.

Yanzu dai kotun ƙolin ta ɗage yanke hukunci kan ƙarar da Jam’iyyar PDP da ɗan takaranta Muhammad Jibrin Barde suka shigar bayan data kammala sauraron dukkanin ɓangarori.

Za a yanke hukunci kan ɗaukaka ƙara na jam’iyyar ta PDP ne a gobe Juma’a.

 

Hafsat Ibrahim