Angudanar da bikin karrama daliban makarantun Gwamnatin da sukayi nasara a fannoni daban daban a birnin Tarayya.

0
18

Taron Wanda aka gudanar dashi a makarantar Gwamnati ta GGSS wuse zone 3 inda makarantun Gwamnati Tarayya suka halarta, A Taron an gabatar da daluban da sukayi zarra a fannoni daban daban, Sannan an bayyana malaman da sukafi kwazo a makarantu, tare da dalibai matan da sukafi kwazo, tare da dalibai mazan da sukafi zarra a karamin matakin sakandire ( Jss) Sannan .

Taron Wanda ya kunshi makarantun Gaba da firamarin Gwamnati dake birnin Tarayya, inda gwarazan kallon kafa suka samu kyaututtuka Sannan aka bawa daliban da suka kasance masu hakaza a bangarorin darussa daban- daban, kyauta wadanda aka zabosu daga makarantu mabambam ta .

 

Abangayaran karatun kimiyyar kuwa makarantar GGSS Garki itace ta farko, sai makarantar Gwamnati Tarayya ta federal government college warzo a mataki na biyu , sai ta karshe wacce tazo a matakin karshe itace makarantar Gwamnati ta GGSSwuse zone 3.

Manyan matane daga fannin Ilmin sun halarta inda Dr danlami Hayyo Wanda ya kasance sakataran Ilmi na Babban birnin Tarayya kuma shine ya wakilci Babban minista na birnin Tarayya. Ya kasance Babban bako na musamman a taron . Daga karshe Dr danlami Hayyo ya bayyana kudurin Minista na bada cikakken gudunwuwa a harkokin Ilmi kamar yadda yake a tanaje- tanajen shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.

 

 

Hafsat Ibrahim