LEMUN KARAS

0
601

Kamar yadda Binciken kimiyya ya bayyana cewa, bayan karin dandano da karas yake karawa abinci yana kuma dauke da sinadarai masu yawa da suka hada da antioxidants, beta-carotene, alpha-carotene, lutein, potassium, vitamin C, vitamin A, fibre da Carotenoids.

Shi karas yanada kyau sosae domin kuwa yana kara inganta lafiyar ido, yana Gyara fatan jiki, yana Taimakawa wurin kiyaye kamuwa da ciwon daji (kansa) da sauransu.

A yau zamu koya maku yadda ake hada lemun karas

ABUBUWAN DA AKE BUKATA SU NE:

 

Karas

Cittah

Sugar

Flavour

abarba

YANDA AKE HADAWA

 

  1. Da farko zamu wanke karas dinmu , ya wanku sosai sai  mu yanka kanana mu zuba a bilenda.
  2. Sai mu wanke cittan mu  itama  a yanka kanana sai a  zuba a bilenda shima abarban a sa a bilenda  a sa ruwa a markada da karas din, yayi laushi.
  3. Sannan sai a tace a sa sugar da flavour.
  4. A juya sosae sae ki sa a firinji yayi sanyi a sha lafiya.

 

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho