LEMUN ZOBO {ZOBO DRINK}

0
204

zobo wani abin sha ne mai dadi da ake sarrafa wa a gidajenmu cikin sauki, mu sha don nishadantuwa.

Sai dai,  bayan ga sarrafa shi dun sha, zobo na da matukar amfani ga lafiyar dan adam.  Saboda haka ne ayau zamu koya maku wannan lemun me cike da amfani ga lafiyar jikin mu.

 ABUBUWAN BUKATA SU NE:

.zobo
. bawon abarba
.water
.sugar
.cocumber
.kanwa
. star anise 
. Cinnamon 
. kankana
YADDA AKE HADA LEMUN ZOBO
 
 1. Awanke zobo yafita tas, sai  ajuye a tukunya azuba ruwa har sai ya haura Kan zobo sai azuba su cinnamon, star anise da bawon abarba da kanwa kadan sabida yarage tsami sai a rufe abarshi ya tafasa na minti uku. 
 
2.Sai a sauke abarshi yawuce daga nan sai a tace.
 
3. Bayan an tace sai ayi blending cocumberda kankana a tace ajuye akai sai asaka sugar.
 
4. Sai  asaka a fridge idan yayyi sanyi sai asha lafiya,
 
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here