‘Mahaukaci’ Ya Kashe Mutane Tara A Adamawa

0
88

 

Wani mai tabin hankali ya kashe akalla mutane tara a jihar Adamawa, kafin daga bisani wasu fusatattun mutane suka yi masa duka har lahira.

 

News Point Nigeria ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da yammacin Laraba a unguwar Libbo, kauyen Kate-Gamji da ke karamar hukumar Sheleng a jihar.

 

Mutumin mai suna Ali Denham, an ce ya fara aiwatar da kisan ne saboda wasu dalilai da ‘yan unguwar ba su sani ba. Rahotanni sun ce ya yi amfani da wuka wajen daba wa wadanda abin ya shafa wuka, ciki har da wata tsoffofi mace da namiji.

 

Wasu fusatattun matasa a ƙauyen sun kewaye Denham bayan ya kashe mutanen, suka kwance masa makami, suka yi masa duka har lahira.

An yi jana’izar gawarwakin wadanda suka mutu a yammacin ranar Alhamis.

Iyalan mutumin da ake zargin sun gudu daga cikin al’umma.

A lokacin da News Point Nigeria ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya-Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya yi alkawarin komawa ga wannan jarida da karin bayani.

Firdausi Musa Dantsoho