Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC ta janye ƙarar da ta shigar tana ƙalubalantar hukuncin da kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano ta yanke a gaban kotun daukaka kara.

0
34

Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC ta janye ƙarar da ta shigar tana ƙalubalantar hukuncin da kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano ta yanke a gaban kotun ɗaukaka ƙara kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

Hukumar ta INEC ta sanar da janye ƙarar ne a cikin wata wasika mai ɗauke da kwanan wata 6 ga watan Oktoba, tare da sa hannun Sulaiman Alkali, Shugaban sashin shari’a na Hukumar.

“An umarceni daga hedikwatar hukumar zabe ta ƙasa domin sanar da cewa babu wani dalilin zuwa kotu domin ɗaukaka ƙara akan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta yi akan kujerar gwamnan Kano”

“Ɓangaren da ke lura da sashen shari’a na Hukumar INEC a matakin ƙasa da kuma babban kwamishinan hukumar mai kula da shiyyar Kano, sun yi umarni da a janye batun ɗaukaka ƙarar tare da miƙa dukkanin wani batu mai nasaba da batun ɗaukaka ƙarar zuwa ofishin hukumar zabe da ke Kano”

 

Daga Fatima Abubakar