Majalisar dinkin duniya ta ayyana 8 ga watan maris a matsayin ranar mata na duniya.

0
23

Fiye da karni guda da ya wuce,mutane da dama na bikin tunawa da zagayowar 8 ga watan maris ta kowace shekara musamman saboda karrama mata a fadin duniya.

Ranar mata ta duniya (wato international women’s day)a takaice ta fara ne daga kungiyar Kwadago,don a san da ita a cikin ranakun shekara-shekara wanda majalisar dinkin duniya ta ware.

An kuma dasa tushenta ne a shekarar 1908,lokacin da mata 15000 su ka yi tattaki a birnin New York ta kadar Amurka domin neman gajeren lokutan aiki,biyan albashi mai kyau da kuma daman kada kuri’a.

Shekara daya tak bayan tattakin,shine majalisar dinkin duniya ta ayyana 8 ga watan maris na kowace shekara a matsayin ranar mata na duniya.

Wata mai fafutukan kare hakkin bil adama Clara Zektin ce ta fara bullo da batun ranar a shekara 1910,a wani babban taron mata na kasa da kasa a birnin Copenhagen,wanda ya samu halaccin mata 100 daga kasashe 17,yayin da suka amince da kudurin.

An fara bikin ranar ne a 1911 a kasashen Austria, Denmark, Jamus da Switzerland. An gudanar da komai a hukumance a shekarar 1975,lokacin da majalisar dinkin duniya ta fara gudanar da bikin a ranar.

Daga Fatima Abubakar.