Majalisar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na PDP, Gwamnoni, Sanatoci Sun Shirya Gaggarumin Zanga-zanga zuwa Ofishin INEC A Yau Litinin

0
28

Kungiyar yakin neman zaben jam’iyyar PDP, Gwamnonin PDP, Sanatoci da dattawan jam’iyyar sun shirya wata gagarumar zanga-zanga zuwa ofishin INEC a yau Litinin, News Point Nigeria  ta tattaro.

A cewar wasikar gayyata, mai dauke da sa hannun daraktan jam’iyyar PDP PCO, Ibrahim Bashir, wadda News Point Nigeria ta samu ta musamman, an shirya gudanar da zanga-zangar ne daga Legacy House, Maitama, Abuja.

Wasikar ta bayyana cewa, rigar wasan zanga-zangar duk baki ce kuma shugaban jam’iyyar ta kasa, Dr Iyrochia Ayu, mataimakin dan takarar shugaban kasa kuma gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyichukwu Okowa, gwamnonin jihar AKWA IBOM, Shugaban PCC, Mista Uger Emmanuel, jihar Sakkwato, Adamawa, Bauchi, Taraba da aka gayyata.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho