Matar dan shugaba Buhari, Yusuf Buhari, watto Zahra Bayero, ta kammala karatun digiri na farko a fannin Architectural Science a jami’ar kasar Birtaniya. Surukarta, Aisha Buhari ta bayyana hakan ta shafinta na sada zumunta a ranar Talata, 20 ga Satumba, 2022.
Inda uwargidan shugaban kasa ta wallafa rubutu kamar haka “Ina taya Misis Zahra B Buhari murnar kammala karatunta na digiri na farko a fannin Architectural Science. Ina muku fatan alheri.”
Ga hotunan bikin kamalawan karatunta:
Daga: Firdausi Musa Dantsoho