Matar Yusuf Buhari, Zahra ta kamala karatunta da first class a fannin Kimiyyar Gine-gine

0
315

Matar dan shugaba Buhari, Yusuf Buhari,  watto Zahra Bayero, ta kammala karatun digiri na farko a fannin Architectural Science a jami’ar kasar Birtaniya. Surukarta, Aisha Buhari ta bayyana hakan ta shafinta na sada zumunta a ranar Talata, 20 ga Satumba, 2022.

Inda uwargidan shugaban kasa ta wallafa rubutu kamar haka “Ina taya Misis Zahra B Buhari murnar kammala karatunta na digiri na farko a fannin Architectural Science. Ina muku fatan alheri.”

Ga hotunan bikin kamalawan karatunta:

Daga: Firdausi Musa Dantsoho