Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Mista Ezenwo Nyesom Wike ya bayyana cewa suna bin hakkinsu na ci gaba da mara wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu baya, ba ta re da la’akari da jam’iyyar da suke ciki ba.
Ministan ya bayyana hakan ne a yayin da yake karbar wata tawagar shugabannin jam’iyyar APC reshen Jihar Ribas, karkashin jagorancin mataimakin shugabanta na kasa na yankin Kudu-maso-Kudu suka kai masa ziyarar taya murna a ofishinsa, jim kadan bayan bayyana nasarar Shugaba Tinubu da Kotun Kolin Najeriya ta yi a ranar Alhamis.
Ministan ya kuma cewa, ba boyayye ba ne a matsayinsa, kuma ba shi da uzuri ga kowa. Ya ce ya tsaya ne kan adalci da gaskiya wajen mara wa Tinubu a matsayin shugaban Najeriya.
Mista Wike, ya kuma jaddada bukatar ‘yan Najeriya da su ci gaba da marawa shugaba Bola Tinubu baya. Ya ce, Tinubu na aiki da niyyar siyasa don daukar matakan da za su dace da duk ‘yan Najeriya.
Ministan ya kara da cewa, “Goyon baya ga Tinubu ya zama dole domin yana da iya aiki da kuma niyyar siyasa don daukar matakan da za su dace da daukacin ‘yan Najeriya, mu ci gaba da mara masa baya.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa a Shiyyar Kudu-maso-Kudu, Victor Giadom, ya ce sun kai ziyarar ne domin taya Wike murnar nadin da aka yi masa tare da yin alkawarin goyon bayan jam’iyyar.
“Mun zo ne domin taya Wike murna bisa nadin da aka yi masa a matsayin ministan tarayyar Najeriya mai kula da babban birnin tarayya.
“Muna kuma gode muku kan goyon bayan da kuka ba dan takararmu na shugaban kasa, Bola Tinubu a zaben da ya gabata, muna rokon ku da ku ci gaba da marawa shugaban kasan baya.
Idan dai ba a manta ba, a Kotun Kolin ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta PEPC ta yanke na cewa dan takara ba ya bukatar samun akalla kashi 25 cikin 100 na kuri’un Babban Birnin Tarayya, kafin ya zama shugaban Najeriya.
Kotun dai ta yanke hukuncin ne kan karar da jam’iyyar adawa ta PDP, da Dantakararta, Atiku Abubakar suka shigar a kan jam’iyyar APC, da Dantakararta, Bola Ahmed Tinubu.
Daga Fatima Abubakar.