RARARA YA ZARGI TSOHON SHUGABAN KASA BUHARI, DA YUNKURIN HALAKA SHI

0
49

– Ya Kuma Ce, Ya Yi Nadamar Tafiya Da Tsohon Shugaban.

Rahotanni daga kafar Sada zumunta ta Soshiyal Midiya sun nuna cewa fitaccen Mawakin Siyasar nan a Nijeriya, Malam Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, ya zargi Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da yunkurin hallaka shi, la’akari da yadda tsohon shugaban ya sa aka janye masa jami’an tsaro, a daidai lokacin da bai kamata ba.

A nazarin da TOZALI TV ta yi, ta gano cewa mawakin ne da kansa ya furta hakan a wani taron manema labarai da ya yi a ofiahinsa, ya kuma sanya a shafinsa na Sada Zumunta na TikTok, inda ya kuma cewa, babu wani abu a cikin gwamnatin tsohon Shugaba Buhari, illa zunzurutun kakubale.

Mawakin ya kuma kara da cewa yayi da na sanin goyawa Tsohon shugaban Nigeria Buhari, baya a lokacin mulkin sa.

Dauda Rara ya tabbatar da cewa tunanin abinda Buhari ya yi ka iya sawa ya kamu da cutar hawan jini, la’kari da shakulatin bangaron da aka yi da shi a mulkin Buhari.

A taron dai, Rarara ya ce, kwana 100n da shugaba mai ci Tinubu ya yi, ta fi shekara Takawas din da Buhari yayi yana mulki.

Sai dai Raran, ya kalubalanci sabuwar Gwamnatin Tinubu, domin kuwa ya ce idan ba ayi musu komai da mutanen sa ba, to kowa zai kama gaban sa.

Mawaki Rara, dai na daya daga cikin wadan da suka marawa Buhari baya a lokacin yakin neman zaben sa, kafin daga baya ya ce, ya yi da na sanin marawa Buharin baya.

 

Daga Fatima Abubakar.