Ranar kwarewar ta matasar duniya,wata kungiya mai zaman kanta zata horar da matasa a koyon sana’o’i daban-daban domin dogaro da kai

0
71

Bikin na bana ya gudana ne a daidai lokacin da ake kokarin farfado da tattalin arziki da zamantakewar al’umma daga annobar Covid-19 da ke da alaka da ‘yan asalin kasar da ke fuskantar kalubale iri-iri.

Mr Isa Muhammed Muhammed wanda a taron na yau da aka kaddamar a Diplomatic Park and Garden da ke Area 1 a Garki,wanda ya wakilci Uwar taron wato Dr Jummai Ahmadu ta yi kira ga matasan da su jajirji wajen dogaro da kai da kuma kokarin yin anfani da abinda suka koya.

A kiyascin UNESCO kusan kashi 70 na matasan duniya na fuskantar matsalar rufe makarantu a duk matakin ilmi.Binciken cibiyoyin TVET da UNESCO,Kungiyar kwadago ta duniya (ILO)da Bankin duniya sun ba da rahoton cewa ilmantarwa a yanzu ita ce hanyar da aka fi sani tare da isar da fasaha.

Tace rashin aikin yi na matasa na kara kawo tabarbarewar tattalin arzikin duniya wanda al’umma ke fuskanta.

Taken taron na bana a bikin ranar fasaha ta matasa ta duniya: ‘Canza fasahohin matasa don gaba”, za a fitar da mahalarta daga kananan hukumomi shida na babban birnin tarayya Abuja don tabbatar da wakilci da kuma hada baki daya.

Don haka gidauniyar ta mayar da hankali ne wajen inganta dimbin matasa ‘yan asalin kasar saboda yuwuwar bunkasar tattalin arzikin kasa da kwanciyar hankali.Yin hakan  zai taimaka musu wurin guje wa aikata laifuka.

Daga Fatima Abubakar