Dan tsohon shugaban kasa, Marigayi Umar Musa ‘Yar’Adua zai daura aure da amaryarsa, Yacine.

0
223

An ruwaito cewa Shehu Yar’Adau daya daga cikin ‘ya’yan tsohon shugaban kasa Umar Musa Ya’Adua na shirin auren amaryarsa, Yacine. Za a daura aurensu ne a ranar Asabar 23 ga watan Yuli a Maiduguri, jihar Borno.

Amarya Yacine ta kasance diya ce ga Hon.Mohammed-Nur Sheriff.

Shehu, mai shekaru 29, ya samu digirin farko a fannin tattalin arziki daga makarantar kasuwanci ta Schellhammer ta kasar Spain sannan kuma ya yi digiri na biyu a fannin hulda da kasashen duniya daga Jami’ar Webster ta kasar Netherlands.

haka zalika amarya Yacine tana da shekaru 22 kuma tana da digiri na farko a fannin Gudanar da Baƙi daga Jami’ar Surrey ta Burtaniya.

DAGA:UMMU KHULTHUM ABDULKADIR