Shin mata suna da warin jiki a lokacin al’adarsu?

0
77

 

Kamshin jikin mace da yadda take jin warin na iya canjawa a lokacin al’adarta.
Al’adar mace tana da sauye-sauyen hormonal da ke yin tasiri a bangarori daban-daban na rayuwarta, tun daga yanayinta na yau da kullum zuwa yanayin barcinta, cin abincin ta, har ma da yanayin take kamshi ko warin jikinta.

Wani abin sha’awa shi ne, akwai jijiyoyi da yawa a cikin wurin jin kamshi na mace fiye da na namiji, wanda ke nuna cewa jin warin Mace ya fi daidai. Wannan ya bayyana dalilin da ya sa mata kullum sun fi maza sanin wari.

Wani bincike na 2019 da aka buga a cikin Hormones and Behavior ya gano cewa mata suna da mafi girman hankali na jin ƙamshi kamar na turare da na maza .
A gefe guda kuma, yawancin mata suna samun warin jiki idan suna cikin haila.

A lokacin jinin haila, an tantance rukunin mata kan kasance da warin hamata a wani bincike da aka yi a jami’ar Charles da ke Prague. Matan da ke da mugun warin jiki su ne waɗanda ke kan al’adar su na wata-wata, a cewar masanin kimiyya Jan Havlieek.
Menene dalilin nazarin halittu na wannan? Wasu mutane sunyi imanin cewa jikinka na iya amfani da warin jiki don nuna haihuwa.

Wasu kuma sun yi imanin cewa wannan warin jikin mai ƙarfi, wanda wasu za su iya zama abin ƙyama, ya taka rawar juyin halitta. Hakan na zama gargadi ga mazan cewa matar ba ta shirya don zama uwa ko saduwa ba.
Lokacin da mace ta ke al’ada, tana buƙatar kulawa da jikinta sosai. Ta hanyar yin wanka akai-akai da kuma yawan amfani da turarrarukan jiki na deodorant.

Firdausi Musa Dantsoho