A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da tsaffin gwamnonin jihar Ribas, Nyesom Wike, da na jihar Kaduna, Mallam Nasir el-Rufai, a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Tsofaffin gwamnonin biyu wadanda aka nada a matsayin ministoci.
Sai dai yayin da Majalisar Dattawa ta tantance Wike kuma ta tabbatar da hakan, Majalisar Dokokin kasar ba ta tabbatar da el-Rufai ba saboda wani rahoton tsaro da ake zargin ya yi.
Tsoffin gwamnonin sun isa gidan gwamnatin a lokuta daban-daban.
Yayin da Wike ya zo da misalin karfe 1:40 na rana, el-Rufai ya shiga bangaren shugaban kasa na Aso Rock da karfe 2 na rana.
Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa ana kokarin ganin majalisar dattawa ta tabbatar da Mallam el-Rufai.
Daga Fatima Abubakar.