Shugaba Tinubu Zai Rantsar Da Sabbin Ministoci A Ranar Litinin

0
14


A ranar litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu zai rantsar da sabbin ministocin da aka ba su mukamai.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ya fitar.

Sanarwar ta ce za a gudanar da bikin ne a dakin taro na fadar gwamnatin jihar da karfe 10 na safe.

Daraktan yada labarai na ofishin SGF, wanda ya sanya hannu kan sanarwar, William Bassey, ya ce ministocin za su zo da baki biyu kowanne.

Tun da farko dai fadar shugaban kasar ta fitar da jerin  sunayen sabbin ministoci da mukamansu.

Firdausi Musa Dantsoho