Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya aika sakon ta’aziya ga sanata Magatakarda Wamako,a bisa rasuwar iyalin sa,Hajiya Atika Wamako.

0
58

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko bisa rasuwar matarsa, Hajiya Atika.

A cikin sakon ta’aziyyar da ya fitar a ranar Litinin, Shugaba Buhari ya ce: Ya samu labarin rasuwar Atika a matsayin babban rashi da ba a iya maye gurbinta. Rasa macen da ta kasance wani muhimmin bangare na rayuwar namiji,  kasancewarta uwar ‘ya’yan shi, yana da matukar zafi da ba za a iya mancewa ba.

“Buhari ya ce,a yayin da kuke alhinin rasuwar matar ka, ina mika sakon ta’aziyyata kan wannan rashin da ba za a iya misalta shi ba. Allah ya gafarta mata kurakuranta, kuma ya saka mata da alhairi. Allah ya ba ku da iyalanku hakuri ya kuma ba ku ikon shawo kan wannan babban rashi. Amin.”

 

Daga Fatima Abubakar.